logo

HAUSA

Manyan kasashen duniya na neman cin gajiyar ci gaban kasar Sin

2023-09-05 17:59:25 CMG Hausa

A farkon wannan mako ne ministan harkokin wajen kasar Italiya Antonio Tajani ya fara ziyara a kasar Sin. Ziyarar da ta zo a daidai lokacin da ake ta tsokaci game da kasancewar kasar cikin shawarar Ziri Daya da Hanya Daya, kasancewarta kasar Turai tilo dake cikin shawarar.

Yayin da shawarar Ziri Daya da Hanya Daya ke cika shekaru 10, kasar Italiya ta kasance cikin wadanda suka ci gajiyarta. Misali kadan daga ciki ya hada da yadda yawan cinikayya tsakanin kasashen biyu ya habaka zuwa kusan dala biliyan 80 daga dala biliyan 50. Haka kuma yawan kayayyakin da Italiya ke shigo da su kasar Sin ya karu da kaso 30 cikin shekaru 5 da suka gabata. Wannan kadai ya nuna yadda Sin take taka gagarumar rawa wajen bunkasa cinikayya da ma tattalin arzikin kasar ta Turai. Haka zalika, ya nuna cewa, duk da yunkurin da wasu kasashen yamma ke yi na neman raba gari da Sin ko rage dogaro da ita, ra’ayin wasu da dama ya bambanta, kuma sun san abun da kasashensu da duniya ke bukata domin samun ci gaba a wannan zamani da ake fuskantar kalubale. Za mu iya gane hakan idan muka yi la’akari da cewa, Antonio Tajani shi ne babban jami’i na 4 daga kasashen kungiyar G7 da ya kawo ziyara Sin a baya-bayan nan.

Irin wannan ziyara da manyan jami’an manyan kasashe ke kawowa kasar Sin, yana kara bayyanawa al’ummar duniya cewa, jita-jitar da ake yadawa ba su da kamshin gaskiya ko kadan, kana ana yinsu ne da zummar bata sunan kasar Sin da kuma kokarin dakile ci gabanta, ganin irin tagomashin da take samu a duniya da ma jajircewarta wajen raya kanta bisa tsayawa da kafarta.

 A yayin tattaunawarsa da ’yan kasuwar kasarsa dake Sin, Tajani ya ce gwamnatinsu na son inganta musu hanyoyin kara shiga kasuwar kasar Sin. Abun nufi, gwamnatin kasarsa na son kara cin gajiyar kasar Sin da ma dimbin damarmakin kasuwanci da bude kofar da take kara yi ga ’yan kasuwa da masu zuba jari na kasashen ketare. Lamarin dake kara jaddada cewa, raba gari da kasar Sin ba abu ne mai yiwuwa ba. Kana su ma manyan kasashen duniya, suna son cin gajiyar ci gaban kasar Sin da dimbin damarmakin da take da su.

Ita dai Sin ta sha nanata cewa, a shirye take ta yayata fasahohinta tare da ba kasashen duniya damar cin gajiyar ci gabanta da tafarkin da ta dauka na zamanintar da kanta.  (Faeza Mustapha)