logo

HAUSA

Da Alamun Japan Ta Debo Ruwan Dafa Kanta

2023-08-30 19:36:04 CMG HAUSA

DAGA Ibrahim Yaya

Tun a ranar 24 ga wannan wata ne, kasar Japan ta fara sakin ruwan dagwalon tashar nukiliyar Fukushima zuwa cikin teku, lamarin da ya gamu da rashin amincewa daga bangarori da dama daga ciki da wajen kasar. Sanin kowa ne cewa, batun amincewa da shirin Japan na zubar da ruwan dagwalon nukiliyar a cikin teku, ba batu ne da wasu kasashe tsiraru za su amincewa ba, musamman karkashin bukatun kasashe na cimma burin siyasa.

A shekarar 2021 ne dai Japan ta bijiro da wannan aniya, bayan da wata girgizar kasar ranar 11 ga watan Maris din a shekarar 2011 da ta lalata tashar nukiliyar Fukushima, tare da haddasa yoyon sinadarin nukiliya, tun lokacin ne kuma aka rika nusar da Japan da ma wadanda suka bayar da shawarar aikata wannan danyen aiki.

Idan ba a manta ba, shi ma taron kasashen nan 7 masu karfin tattalin arziki a duniya wato G7 da ya gudana a kasar ta Japan, bai goyi bayan shirin kasar na zubar da ruwan dagwalon a cikin teku ba, saboda illarsa ga yanayin teku da tsaron abinci da ma lafiyar daukacin bil-Adama, amma bangaren Japan ya ci gaba da yin kunnen uwar shegu da neman kare kansa ta kowace hanya, wai don saboda arahar wannan tsari, wanda masu iya magana ke cewa, ba ta ado.

Abin takaici shi ne, yadda Japan ta dage cewa, wai shirin nata ya samu amincewar Amurka, da wasu karin kasashen ma yaudarar kai ne kawai, saboda wannan danyen aiki zai shafi lafiyar al’ummar duniya ne baki daya.

Ya kamata Japan ta fahimci cewa, akwai kasashe kusan 200 a duniya, kuma kalilan ne suka bayyana amincewa da shirin nata. Hasali ma dai mafi yawan kasashen duniya ciki har da al’ummar Japan da kansu, sun bayyana adawa, da rashin gamsuwa da zubar da ruwan dagwalon nukiliyar cikin teku.

Gaskiyar al’amari shi ne bai kamata Japan ta kawar da kai daga gaskiya ba, balle kuma ta rika yaudarar kanta". Wannan ya kara nuna cewa, Japan ba ta damu da lafiyar jama’arta ba, balle ma ta damu da lafiyar al’ummar duniya. Abin dake tabbatar da cewa, Japan ta debo ruwan dafa kanta da kanta.

Yanzu dai kasar Sin ta dauki matakin kare lafiyar jama’arta da ma na ragowar kasashen duniya, ta hanyar haramta shigo da kayan ruwa daga Japan, tun lokacin da Japan din ta fara sakin ruwan dagwalon nukiliyar a cikin teku.

Masharhanta na cewa, zubar da ruwan dagwalon nukiliyar da Japan ta yi, ko shakka babu zai shafi muhallin teku da lafiyar bil adama. Kuma mataki ne na nuna karfin iko, da yin watsi da damuwar sassan kasa da kasa, da martaba moriyar kai, da yin fatali da moriyar sauran sassan kasa da kasa. Amma kowa ya debo da zafi aka ce bakinsa. (Ibrahim Yaya)