logo

HAUSA

Babu Kasar Da Za Ta Samu Ci Gaba Ba Tare Da Tabbatuwar Tsaro Ba

2023-08-29 19:51:17 CMG HAUSA

DAGA Faeza Mustapha

 

An fara gudanar da taron dandalin tsaro da zaman lafiya na Sin da Afrika karo na 3, daga jiya Litinin zuwa ranar Asabar, a wani yunkuri na tabbatar da tsaro da kaucewa babakeren manyan kasashen yamma.

Har kullum Sin ta kasance mai taka rawar gani game da abubuwan da suka shafi ci gaban Afrika; ciki har da tsaro, bisa girmama muradu da ’yancin kasashen Afrika kana  ba tare da gindaya wasu sharudda na siyasa ba. Kasashen Afrika sun riga sun san yadda kasashen yamma suke fakewa da tallafin tsaro wajen tsoma baki cikin harkokinsu na gida kuma ba tare da tabuka abun kirki ba, sai ma yi musu zagon kasa da ta’azzara yanayin da suke ciki maimakon samar da zaman lafiya.

Kasar Sin ta yi kuma an gani sabanin wadancan kasashe. Wato ta dauki matakan tabbatar da tsaro bisa kalubalen da ta fuskanta, kuma za ta iya bugin kirji ta ce lallai kwalliya ta biya kudin sabulu, inda ta shafe shekaru da dama ba tare da fuskantar harin ta’addanci ko wasu munana laifukan tsaro ba, shin kasashen yamma za su iya alfahari kamar Sin?

Matsalolin tsaro da kasashen Afrika suke fuskanta da suka hada da na ta’addanci da kabilanci da na ’yan aware, sun yi kama da irin wanda Sin ta taba fuskanta, kuma zuwa yanzu, matsalolin sun zama tarihi a kasar. Bisa wadannan dalilai nake ganin, babu wadda ta fi dacewa ta koyar da dabarun tabbatar da tsaro kamar kasar Sin, la’akari da dimbin kamaceceniyar dake akwai tsakaninta da kasashen Afrika. Na ziyarci bangarori da dama na kasar Sin, kuma na ganewa idona dimbin ci gaban da kasar ta samu, wanda ba ya rasa nasaba da tabbatuwar tsaro da zaman jituwa tsakanin kabilu daban-daban na kasar. Don haka, babu wani dalili da zai hana kasashen Afrika tabbatar da tsaro muddun suka yi watsi da yaudarar kasashen yamma tare da dauka da aiwatar da darasin da Sin za ta samar, lamarin da kuma zai kai su ga samun ci gaban da suke muradi. (Faeza Mustapha)