logo

HAUSA

Tarihi zai dorawa Japan alhakin sakin gurbataccen ruwan nukiliya zuwa teku

2023-08-24 22:00:38 CMG Hausa

Da misalin karfe 1 na ranar Alhamis din nan ne, bisa agogon wurin, gwamnatin kasar Japan ta fara sakin gurbataccen ruwan tashar nukiliyar Fukushima a cikin teku wanda al’ummomin duniya masu dimbin yawa suka nuna adawa da matakin. Wannan rana ta zama ranar bala’i ga yanayin tekun duniya. Kuma gwamnatin kasar Japan ta zama mai lalata muhallin halittu da ma gurbata tekun duniya.

Shi ne karo na farko da aka saki gurbataccen ruwan nukiliya zuwa cikin teku da gangan, bayan bil’adama sun yi amfani da makamashin nukiliya ta hanyar zaman lafiya. Masana sun yi hasashe cewa, ya zuwa yanzu, kasar Japan tana da gurbataccen ruwan nukiliya kusan ton miliyan 1.3, kuma da alamun za a shafe shekaru 30 zuwa 50 ana sakinsu zuwa teku. Bayanai na nuna cewa, watakila gurbataccen ruwan nukiliya zai mamaye kusan duk fadin tekun Pasifik.

Sanin kowa ne cewa, dalilin da ya sa gwamnatin kasar Japan ta zabi shirin sakin gurbataccen ruwan nukiliya zuwa teku a cikin shirye-shriye guda biyar, shi ne tana ganin wannan shiri ba zai lakume kudi da yawa ba kuma yana da sauki wajen aiwatar da shi.

Kasar Japan ta gamu da hadari, amma ta kawo wa duniya baki daya wannan hadari, wanda ya sanya kasa da kasa cikin tashin hankali. Firaministan kasar Japan Fumio Kishida ya sanar da cewa, zai dauki alhakin shirin sakin gurbataccen ruwan nukiliya zuwa teku. Amma a gaskiya, ta yaya 'yan siyasar kasar Japan za su iya "daukar alhakin" wannan "hadarin" wanda ya kasance kamar wani harin da aka kai wa duk duniya, amma ba shi da shirin share fage, kuma babu hanyar rage asararsa? Kuma me za su fadawa zuriyoyinsu?

Tarihi zai dorawa Japan alhakin sakin gurbataccen ruwan nukiliya zuwa teku. (Safiyah Ma)