logo

HAUSA

Lai Ching-te dan tada hargitsi ne

2023-08-19 18:46:17 CMG Hausa

Jiya Jumma’a, mataimakin jagoran yankin Taiwan na kasar Sin Lai Ching-te, ya gama yada zango a kasar Amurka, tare da koma yankin Taiwan. Kafin da kuma bayan yada zangon sa a kasar Amurka, al’ummomin yankin Taiwan da Sinawa dake kasar Amurka, sun yi Allah wadai da abun da ya aikata da kakkausan harshe, inda suka nuna adawa da cewa “Ba za a taba raba yankin Taiwan daga kasar Sin ba”, kuma “Duk wanda ke goyon bayan raba yankin Taiwan daga kasar Sin ba zai cimma nasara ba”. Kaza lika a wannan karo, Amurka ba ta yi masa maraba da zuwa sosai ba.

Cikin dogon lokaci da ya gabata, Lai Ching-te yana ta kokarin hana dunkulewar kasar Sin baki daya, wanda hakan ya nuna cewa, shi mutum ne mai burin tada hargitsi, dake neman bata yanayin zaman karko a yankin Taiwan.

Babban burinsa na yada zango a kasar Amurka, shi ne neman goyon bayan bangaren Amurka, yayin zaben shugabannin da za a gudanar a yankin Taiwan, da kuma tallata mugun ra’ayin raba yankin Taiwan daga kasar Sin cikin kasashen duniya. Tabbas hakan zai haddasa illa ga dangantakar dake tsakanin kasar Sin da kasar Amurka. Kuma Lai Ching-te, bai cimma burinsa ba a wannan karo, domin a ganin gwamnatin kasar Amurka, ba shi da amfani.

Bugu da kari, wasu masu sa ido na cewa, yanzu haka akwai karin mutanen yankin Taiwan dake ganin cewa, ra’ayin “raba yankin Taiwan daga kasar Sin”, zai iya haddasa tabarbarewar yanayin zaman karko a yankin na Taiwan, wanda ya saba wa fatan al’ummomin kasar Sin.

Bugu da kari, ana nuna adawa da wadanda suke neman raba kasar Sin, yayin da neman dunkulewar kasar Sin bai daya, ya dace da moriyar jama’ar kasar Sin. Gwamnatin kasar Sin tana fatan samar da damammaki na neman dunkulewar kasar Sin bai daya, a sa’i daya kuma, ko kadan ba za ta jurewa ayyukan masu neman raba yankin Taiwan daga kasar Sin ba.  (Mai Fassarawa: Maryam Yang)