logo

HAUSA

Yadda Sinawa ke kokarin sayen hidimomi na haifar da alfanu ga manyan kamfanonin kasa da kasa

2023-08-16 10:50:56 CMG Hausa

Wasu alkaluman da gwamnatin kasar Sin ta sanar da su a jiya Talata sun nuna cewa, tattalin arzikin kasar na ci gaba da farfadowa, yayin da fannin sayen hidimomi da ake yi ya karu sosai. An ce, cikin watanni 7 na farkon bana, yawan kudin da Sinawa suka kashe don neman samun hidimomi daban daban ya karu da kashi 20.3% bisa na makamancin lokacin bara. Yayin da kudin da aka kashe wajen sayen kayayyaki ya karu da kashi 7.3%.

Fannin kashe kudi da sayayya wani muhimmin bangare ne dake ba da damar ci gaban tattalin arziki, saboda haka ana sa ran ganin farfadowar bangaren sayayya a kasar Sin, ya taimakawa kokarin daidaita yanayin tafiyar hawainiya da tattalin arzikin duniya ke ciki.

Ban da haka, sauyawar yanayin da aka samu game da fannin sayayya a kasar Sin, wanda ya dogara kan sayen kayayyaki a baya, amma yanzu haka ya fara mai da hankali kan dukkan bangarorin kayayyaki da hidimomi, za ta haifar da sabbin damammaki na samun ci gaba ga manyan kamfanonin kasa da kasa.

Haka zalika, yadda ake samun wani yanayi na tabbas dangane da manufofin tattalin arziki na Sin, shi ma wani muhimmin abu ne da manyan kamfanonin ke dauka da daraja. Yanayi na tangal-tangal da ake fama da shi a duniya ya kan sanya wasu kasashe dake yammacin duniya gyara manufofinsu a fannin tattalin arziki. Sai dai a nata bangare, kasar Sin tana kokarin tabbatar da dorewar manufofinta, ta yadda ‘yan kasuwan kasashen waje ba za su shiga cikin damuwa ba.

Dangane da batun, za mu iya daukar bangaren sayayya a matsayin wani misali, inda a wajen taron gwamnatin kasar Sin game da aikin raya tattalin arziki, da ya gudana a karshen shekarar bara, aka jaddada bukatar baiwa aikin farfado da inganta bangaren sayayya fifiko, sa’an nan zuwa bana, sai a gabatar da jerin matakai don sa kaimi ga bangaren sayayya. Ta haka ana iya ganin wani yanayi na tabbas da manufofin kasar Sin ke haifarwa tattalin arzikin duinya. Kana amfanin wadannan manufofi shi ma ya bayyana sosai. (Bello Wang)