logo

HAUSA

Matakin Amurka na neman takaita zuba jari a kasar Sin illata kai ne

2023-08-11 11:38:47 CMG Hausa

A jiya ne shugaban kasar Amurka Joseph Biden, ya ba da umarnin sake duba yadda ake zuba jari a kasashen waje, da takaita zuba jari ga sassan na’urorin laturoni na “semiconductor”, da kananan na’urorin lantarki, da fasahohin sadarwa, da fasahohin kirkirarriyar basira ko AI a kasar Sin.

To sai dai kuma bangaren tattalin arziki na kasar Amurka, ya nuna damuwa ga wannan mataki. Kungiyar makera sassan na’urorin laturoni na “semiconductor” ta kasar Amurka, ta ce za ta bada ra’ayinta, tare da fatan za a ba kamfanonin matattarar bayanai ta “microchip” na kasar Amurka, damar shiga manyan kasuwannin duniya ciki har da kasar Sin.

Bugu da kari, kungiyar zuba jari ta kasar Amurka, ta ce tana maida hankali kan wannan batu, don magance mugun tasirin da hakan zai yi ga masu zuba jari na kamfanonin kasar Amurka.

Manazarta sun yi nuni da cewa, bayar da wannan umurni ya yi kama da yunkurin siyasa, wanda ya shaida mummunan yanayin siyasar gwamnatin Amurka mai ci. A hannu guda kuma, za a gudanar da zaben shugaban kasar Amurka a shekarar badi, don haka gwamnatin Biden ke maida matakan yiwa Sin matsin lamba a matsayin wata hanyar neman kuri’un goyon baya, don haka ne ma ta gabatar da matakan takaita zuba jari a kasar Sin.

Ko shakka babu akwai tsarin aiwatar da hada hadar tattalin arziki, wanda basirar siyasa ba za ta iya dakatarwa ba. Don haka ya kamata ‘yan siyasar kasar Amurka, su daina yin amfani da basirar siyasa, su saurari ra’ayoyi daga bangarori daban daban, su kuma tsaida kuduri mai dacewa da tsarin tattalin arziki. Matakin kasar Amurka a wannan fanni ba zai hana bunkasuwar kasar Sin ba, kana zai illata ita kan ta Amurka. (Zainab)