logo

HAUSA

Ci gaban kasar Sin abun koyi ne ga kasashen Afrika

2023-08-09 09:43:53 CMG Hausa

Zaunannen wakilin Tarayyar Afrika (AU) a kasar Sin Rahamtalla Osman, ya ce kasar Sin ta kawo gagarumin sauyin wajen raya kanta, abun da ya zama misali ga kasashen Afrika.

Rahamtalla Osman ya bayyana haka ne yayin wata liyafa jiya a birnin Beijing, wadda kungiyar ’yan kasuwar Afrika mazauna kasashen ketare (ADBC) ta shirya, domin tattauna hanyoyin bunkasa ci gaban nahiyar Afrika.

Jakadan na AU ya kara da cewa, Sin ta bude kofofinta ga kasashen Afrika da al’ummarsu, abun da ya kamata ya karfafa musu gwiwa wajen karfafa ci gaban nahiyar Afrika. Ya kara da cewa, AU tana karfafa hadin gwiwarta da Sin, lamarin da zai ba Afrika damar samun dabarun Sin na raya kanta da fatattakar talauci.

A nasa bangare, jakadan Nijeriya a kasar Sin Baba Ahmed Jidda, ya ce kyautata hadin gwiwar nahiyar Afrika da Sin, za ta kawo manyan sauye-sauye a nahiyar. Ya kara da cewa, yayin da taron BRICS ke karatowa a kasar Afrika ta Kudu a wannan wata, ya shawarci gwamnatin kasarsa ta yi amfani da wannan dama wajen cin gajiyar kungiyar har ma da kokarin zama mamba.

Shi kuwa shugaban kungiyar ADBC Kay Gabriel ya ce, 

“Dalilin kafa wannan kungiya shi ne, karfafawa ’yan Afrika mazauna ketare gwiwar zuba jari da taimakawa kokarin da gwamnatocin Afrika ke yi wajen inganta zuba jari da samar da aikin yi ga matasa da yaki da talauci. A ganinmu, ’yan Afrika mazauna ketare na iya yin kyakkyawan tasiri a nahiyar ta hanyar amfani da wadatar da suke da ita.  Kuma abu mafi muhimmanci shi ne hada gwiwa da kwararru dake wajen nahiyar domin inganta sabbin kirkire-kirkire a Afrika.”

Bugu da kari, ya bukaci ’yan Afrika mazauna kasar Sin su kyautata hulda tsakanin Sin da kasashensu, haka kuma su yi kokarin jan hankalin ’yan kasuwar kasar domin su zuba jari a kasashen Afrika.

Liyafar ta jakadun Afrika dake kasar Sin, ta samu halartar jakadun kasashe da dama na Afrika dake kasar Sin, da ’yan kasuwa na Sin da Afrika da dalibai, da kwararru daga bangarorin biyu. (Fa’iza Mustapha)