logo

HAUSA

Kamfanin gine-gine na CBC zai gudanar da aikin gina kwalejin horas da jami’an Kwastam a jihar Ogun

2023-08-09 09:09:56 CMG Hausa

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta baiwa kamfanin gine-gine na CBC kwangilar gina katafaren kwalejin horas da jami’an hukumar kwastam a jihar Ogun dake kudancin kasar.

A jiya Talata ne mukaddashin shugaban hukumar kwastam na kasa tare da wakilan  gwamnatin jihar ta Ogun suka kaddamar da aikin ginin a fili mai fadin kadada 100 kuma za a  kammala aikin a tsawon shekaru 4.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto. 

Mukaddashin shugaban hukumar kwastam ta tarayyar Najeriya Bashir Adewale Adeniyi ya ce samuwar kwalejin a wannan waje ya dace matuka saboda kusancinsa da filin jirgin saman dakon kayan amfanin gona wanda ake daf da kammala aikinsa a karamar hukumar Ikenne a jihar ta Ogun.

Shugaban hukumar ta kwastam ya ja hankalin kamfanin da zai gudanar da aiki cewa,

“Ba ma fatan cewa dai a tsakanin tarewarmu a wannan kwaleji da kuma kammala aikin filin jirgin saman ya dauki lokaci mai tsawo, muna son aikin ya rika tafiya kafada da kafada da na filin jirgin saman, na san cewa kasancewar jami’an kwastam a wannan waje zai amfani filin jirgin, haka kuma mu ma za mu ci gajiya sosai daga yin makwaftaka da filin jirgin.”

Da yake gabatar da jawabinsa, darkatan kamfanin na CBC Mr Shi Hongbing ya ce, zabar kamfanin a matsayin wanda zai gudanar da ginin, abun farin cikin ne matuka kasancewar akwai kamfanonin da yawa da suka nuna bukata.

“Da ma dai mun jima muna jiran wannan rana da za a mika mana ragamar gudanar da wannan aiki, kuma ba za mu dauki wani lokaci ba za mu fara gudanar da wannan muhimmin aiki gadan gadan, muna da kwarin gwiwar cewa za mu kammala aiki a iya wa’adin da aka dibar mana.”

A jawabinsa yayin bikin mika kwangilar, kwamashinan aiyuka na jihar Ogun Injiniya Ade Akinsanya ya ce, a farkon shekarar badi  za a kammala filin jirgin saman dakon kayan amfanin gonar, domin a yanzu haka an ci kaso 90 na adadin aikin. (Garba Abdullahi Bagwai)