logo

HAUSA

Shugabannin da suka yi juyin mulki a Niger sun hana tawagar ECOWAS shiga kasar

2023-08-09 10:02:52 CMG Hausa

Kafar yada labarai ta AFP ta ruwaito shugabannin da suka yi juyin mulki a Niger, sun shaidawa kungiyar raya tattalin arzikin yammacin Afrika ECOWAS cewa, ba za su iya karbar tawagar kungiyar a birnin Yamai ba, saboda dalilai na tsaro.

A cewar AFP, wata wasika da ma’aikatar harkokin wajen Niger ta aikewa ECOWAS a Niamey ta ce bisa la’akari da yanayi na fusata da al’umma ke ciki biyo bayan takunkuman da ECOWAS ta kakabawa kasar, bai dace a karbi bakuncin tawagar ba saboda hakan na bukatar yanayi na tsaro da kwanciyar hankali. (Fa’iza Mustapha)