logo

HAUSA

Najeriya ta tsara harajin kaso 18 don cimma mizanin GDPn ta

2023-08-09 11:03:37 CMG Hausa

 

Shugaban kasar Najeriya, Bola Tinubu ya bayyana a cewa, Najeriya ta sanya kashi 18 cikin 100 na haraji a matsayin mizanin GDPn kasar, a cikin shekaru uku masu zuwa, a wani mataki na rage harajin da ake karba a kasar dake zama mafi yawan al’umma a nahiyar Afirka.

A yayin da yake jawabi a wajen kaddamar da kwamitin da shugaban ya nada kan manufofin kasafin kudi da sake fasalin haraji a Abuja, babban birnin kasar, shugaba Tinubu ya ce an dauki matakin ne, domin inganta matakan tara kudaden shiga da kuma yanayin kasuwanci a kasar.

Ya ce, manufar ita ce canza tsarin harajin kasar, don tallafawa ci gaba mai dorewa. Yana mai cewa idan babu kudaden shiga, gwamnati ba za ta iya samarwa al’ummarta isassun kayayyakin more rayuwa ba. (Ibrahim)