logo

HAUSA

Wata babbar tawagar ministocin kasashen Burkina Faso da Mali ta kawo ziyara a Yamai

2023-08-08 14:09:18 CMG Hausa

Wata babbar tawagar ministocin kasashen Burkina Faso da Mali ta samu tarbo a ranar jiya Litinin 7 ga watan Augustan shekarar 2023 a filin jiragen saman kasa da kasa na Diori Hamani dake birnin Yamai daga janar din rundunoni Salifou Modi, mamba na kwamitin kiyayewa da ceto kasa na CNSP.

Daga birnin Yamai, abokin aikimu Mamane Ada ya aiko mana da wannan rahoto. 

Ita dai tawagar kasar Mali na karkashin jagorancin ministan kasa, kuma kakakin gwamnati, kanal Abdoulaye Maiga tare da rakiyar ministan tsaro, kanal  Sadio Camara, yayin da kuma tawagar kasar Burkina Faso take karkashin jagorancin ministan kasa da tsarin rarraba jihohi da tsaro Emile Zerbo da kuma Mahamadou Sana, karamin ministan dake kula da tsaro. 

Wadannan tawagogi biyu sun samu tattaunawa tare da shugaban kasa, kuma shugaban kwamitin soja na CNSP, birgadiye-janar Abdouramane Tchiani a fadar shugaban kasa dake nan birnin Yamai. 

Haka zalika, bangarorin biyu sun yi zaman taro da zummar kara rubanya karfinsu ta sararin samaniya da ta kasa tsakanin kasashen uku, domin maida martani nan take da zaran an kawo ma kasar Nijar hari. Kasar Nijar dai na raba iyaka da kasar Burkina Faso da kuma kasar Mali, inda kusan al’umomin kasashen uku na mu’amala da junansu tun fil azal, ke nan dole su kasance tsintsiya madaurinki daya domin kare kansu daga kungiyoyin ’yan ta’adda da kuma duk wata barazana, a cewar wakilan kasashen biyu a gaban takwarorinsu na kasar Nijar. 

A nasa bangaren, shugaban kwamitin soja na CNSP bai yi kasa a gwiwa ba domin kawo godiya da sunansa da kuma sunan ’yan Nijar baki daya bisa ga jan namijin kokari da nacewa na kasashen Burkina Faso da Mali suka yi wajen kawo gudunmawarsu ga kasar Nijar domin kare ta daga matakin kungiyar CEDEAO ko ECOWAS na yin amfani da karfin soja domin maido tsarin demokaradiyya da shugaba Mohamed Bazoum bayan juyin mulkin ranar 26 ga watan Yulin shekarar 2023.

Mamane Ada, sashen hausa na CRI daga Yamai a jamhuriyar Nijar.