logo

HAUSA

An nada Ali Mahamane Lamine Zeine a matsayin sabon faraministan Nijar

2023-08-08 09:27:52 CMG Hausa


Sabbin hukumomin sojan kasar Nijar na kwamitin CNSP a karkashin jagorancin birgadiye-janar Abdrouhamane Tchiani ya sanya hannu kan kudurin nada sabon faraministan kasar Nijar bayan wani zaman taronsa a fadar shugaban kasa dake birnin Yamai a ranar jiya Litinin 7 ga watan Augutan shekarar 2023. Ko wanene wannan sabon faraministan kasar Nijar din?

Daga birnin Yamai wakilinmu Mamane Ada ya aiko mana da wannan rahoto.

Shi dai Ali Mahamane Lamine Zeine mai shekaru 58 a duniya, an haife shi a Zinder a shekarar 1965, masanin tattalin arziki ne, kuma dan siyasa na jam’iyar MNSD-NASARA, inda kuma a lokacin mulkin Mamadou Tandja ya rike kujerar ministan kudi daga ranar 24 ga watan Oktoban shekarar 2003 zuwa watan Fabrairun shekarar 2010. Tsohon ministan kudi, Lamine Zeine na a yanzu haka wakilin bankin cigaban Afrika cewa da BAD a kasar Chadi. Kwamitin kiyayewa da ceto kasa na CNSP ya zabi Lamine Zeine bisa la’akari da kwarewarsa ta fannin tattalin arziki, da kuma kwarewarsa kan dangantakar kasa da kasa, da kasancewarsa mutum mai dattako da kuma son aiki da kishin kasarsa. A cewar masu fashin baki tsohon ministan kudin Mamadou Tandja zai yi kokarin maido da ci gaban tattalin arzikin kasar Nijar da ya kasance cikin mawuyacin hali yau fiye da shekaru goma. Yan Nijar da dama ne suka yi maraba da nada Ali Mahamane Lamine Zeine a matsayin sabon faraminista na mulkin rikon kwarya na kwamitin soja na CNSP. Yanzu abin da ’yan Nijar suke jira shi ne na nada sabbin ministocin da za su taimaka masa wajen tafiyar da aikin gwamnatinsa nan ba da jimawa ba.

Mamane Ada, sashen hausa na CRI daga Yamai a jamhuriyar Nijar