logo

HAUSA

Chengdu: Yadda aka hada fasahohin zamani da al’adu cikin gasar wasannin daliban jami’o’i ta duniya

2023-08-08 09:09:37 CMG Hausa

Masu kallonmu, yau Talata 8 ga wata, za a kammala gasar wasannin motsa jiki ta daliban jami’o’in kasa da kasa ta lokacin zafi karo na 31 a birnin Chengdu na kasar Sin. Dakunan motsa jiki masu kyau, da fasahohin zamanin da ake amfani da su a gasar ta wannan karo, sun burge ’yan wasan kasashen duniya kwarai da gaske.