logo

HAUSA

Muisha: Likitocin kasar Sin jarumai ne

2023-08-08 15:21:34 CMG Hausa

A shekaru 10 da suka gabata, wani matashi mai suna Muisha Mbikyo Bienvenue daga Kongo(Kinshasa) ya zo kasar Sin don koyon ilimin likitanci. A lokacin, labaran likitocin kasar Sin dake aikin ba da agaji a kasashen waje da dama sun burge shi kwarai da gaske, abin da ya kara fahimtar da shi kan yadda mutum zai iya zama wani kwararren likita. A cikin shirinmu na yau, za mu ji labarin Muisha, dan kasar Kongo(Kinshasa)dake dalibta a kasar Sin.