logo

HAUSA

MDD ta bayyana damuwa game da yanayin Niger

2023-08-08 10:21:01 CMG Hausa

Sakatare janar na MDD Antonio Guterres, ya bayyana damuwa game da gazawa wajen mayar da kundin tsarin mulki a Niger.

Mataimakin kakakin MDD Farhan Haq, ya ruwaito Antonio Guterres na bayyana damuwa game da yadda har yanzu ake ci gaba da tsare shugaba Mohammed Bazoum da kuma gazawa wajen mayar da kundin tsarin mulkin kasar.

Kakakin ya bayyana a jiya cewa, Antonio Guterres ya jaddada cikakken goyon bayansa ga kokarin da kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika (ECOWAS) ke yi na shiga tsakani. Ya kuma nanata bukatar gaggawa ta tabbatar da ayyukan jin kai na ceton rayuka na gudana ba tare da tangarda ba, haka kuma jiragen sama na MDD masu hidimar jin kai dake bayar da damar shiga muhimman wurare masu nisa a Niger, na samun damar zirga-zirga, tare da ci gaba da hidimtawa wadannan al’ummomi.

Bugu da kari, manzon musamman na sakatare-janar na MDD a yankin yammacin Afrika da Sahel, Leonardo Santos, ya je Nijeriya domin nuna goyon baya ga masu ruwa da tsaki na yankin. (Fa’iza Mustapha)