logo

HAUSA

Afrika ta kudu ta shirya domin karbar bakuncin taron BRICS

2023-08-08 10:39:48 CMG Hausa

Gwamnatin Afrika ta kudu, ta ce ta shirya tsaf domin karbar bakuncin taro karo na 15 na kasashen BRICS masu samun saurin ci gaban tatatlin arziki, wanda aka dade ana dako.

Ministar kula da harkokin waje da hadin gwiwa ta kasar Naledi Pandor ce ta bayyana haka a jiya Litinin, yayin da take yi wa manema labarai bayani game da shirye-shiryen da kasar ta yi domin taron, wanda zai gudana daga ranar 22 zuwa 24 ga watan nan na Augusta.

A cewar ministar, shugaban kasar Cyril Ramaphosa, da kan shi ya tabbatar da shirin kasar na karbar bakuncin taron na BRICS karo na 15 a Sandton dake Johannesburg. Haka kuma ya gayyaci shugabanni 67 daga kasashen Afrika da sauran kasashe masu tasowa domin halartar taron BRICS da Afrika da tattaunawar kasashen BRICS da karin kasashe. 

Taken taron na BRICS da Afrika ta Kudu za ta karbi bakuncinsa shi ne, “BRICS da Afrika: Hadin gwiwa domin gaggauta samun ci gaba tare, ci gaba mai dorewa da huldar kasa da kasa da dukkan bangarori.”(Fa’iza Muhammad Mustapha)