logo

HAUSA

Majalissar mulkin rikon kwarya a Sudan ta fitar da tsarin kawo karshen yaki

2023-08-08 10:22:07 CMG Hausa

Mataimakin shugaban majalissar mulkin rikon kwarya a Sudan Malik Agar, ya gabatar da tsarin da suka amincewa, na kawo karshen yaki a kasar.

Agar wanda ya gabatar da shirin majalissar ta soji a jiya Litinin, a shafinsa na Facebook, ya ce sun amince da raba tsakanin dakarun dake dauki ba dadi da juna, da amincewa a gabatar da kayayyakin jin kai, da kare rayukan fararen hula. Kazalika sun amince su fara wani yunkurin siyasa, wanda zai mayar da hankali ga kafuwar kasa maimakon rarraba iko.

Jami’in ya kara da cewa, “Aiwatar da mabanbantan manufofi na iya haifar da illa ga yunkurin wanzar da zaman lafiya da tsawaita yaki. Akwai bukatar kaucewa aiwatar da manufofi daban daban a lokaci guda, domin cimma nasarar kawo karshen yakin soji da ake fama da shi a Sudan”. (Saminu Alhassan)