logo

HAUSA

Najeriya: Sake daukar tsauraran matakan tsaro kan iyakokin Najeriya da Nijar na wani dan lokaci ne kawai

2023-08-08 09:23:36 CMG Hausa

Najeriya ta kara daukar tsauraran matakan tsaro a kan iyakokinta da Jamhuriyyar Nijar, inda aka dakatar da shige da ficen jama’a da kuma na kayayyaki a wani mataki na takurawa sojin Nijar da su mayar da mulkin ga hannun shugaban Mohamed Bazoum.

Tun daga jiya Litinin, hadin gwiwar jami’an tsaron soji da na hukumar shige da fice da hukumar Kwastam da kuma jami’an tsaron DSS suka mamaye manyan iyakokin Najeriya da kasar ta Nijar bisa yarjejeniyar kungiyar Ecowas.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto. 

Iyakokin da aka jibge jami’an tsaro sun hada da Kamba dake jihar Kebbi, Illela a jihar Sakkwato, Jibiya, Maradi, Zango, Mai’aduwa da Kaita duk a jihar Katsina.

Sauran su ne Gurbin Bore dake Zurmi a jihar Zamfara da kuma Babura da Maigatari a jihar Jigawa.

Haka abun yake kuma a jihohin dake arewa maso gabashin Najeriya wanda suke kan iyaka da jamhuriyar Nijar.

A lokacin da yake jawabi bayan da ya ziyarci kan iyakar dake Illela a jihar Sakkwato, shugaban hukumar kwastam ta Najeriya Bashir Adewale Adeniyi ya ce, rufe kan iyakokin da aka yi ko kadan ba shi da wata alaka dake da nufin gallazawa ’yan Najeriya.

Abdullahi Maiwada shi ne jami’in yada labaran hukumar kwastam a tarayyar Najeriya ya yi mana karin haske ta wayar tarho a game da jawaban na shugaban hukumar ta kwastam, 

“A yanzu sai an yi hakuri da yanayi an san cewa mutane za su ji zafin wannan abu amma kuma abun an yi shi ne domin ci gaban Afrika gaba daya da kuma ci gaban demkoradiyya.”

To ganin akwai iyakoki da dama tsakanin Nijar da Najeriya da wata hukuma ta sani da kuma wanda ba ta sani ba, wane irin matakan tsaro kuka dauka a kan sauran kan iyakokin da ake shigowa ba bisa ka’ida ba?

“Ai tun farko shugaban hukumar Kwastam ya sha alwashin kula da kan iyakoki gaba daya ba wai sai iyakar Nijar ba da Najeriya har da wadanda suke a kan iyakarmu da jamhuriyar Benin, kuma muna kara yin kira ga jama’a cewa misali idan mutum ya samu karaya aka zo dora shi zai ji zafi to amma wannan zafin da yake ji zafi ne na wani dan lokaci domin ya samu.”(Garba Abdullahi Bagwai)