logo

HAUSA

Sojojin Nijar sun sanar da rufe sararin samaniyar kasar

2023-08-07 10:19:04 CMG Hausa

Da yammacin jiya Lahadi agogon kasar ne, rundunar sojin Jamhuriyar Nijar ta ce sojojin kasashen waje na shirin kai wa Nijar din hari. Domin mayar da martani kan yiwuwar kai mata hare-hare, hukumomin kasar sun sanar da rufe sararin samaniyar kasar har sai illa masha Allahu.

A cewar sojojin, duk wani yunkuri na keta hurumin sararin samaniyar kasar ta Nijar, to, zai gamu da martani mai karfi nan take. (Ibrahim)