logo

HAUSA

An gargadi masu amfani da iskar gas na LPG a ababen hawa da injunan wuta maimakon gas din CNG a jihar Kano

2023-08-07 09:27:22 CMG Hausa

Hukumar kashe gobara ta jihar Kano dake arewacin Najeriya ta bayyana damuwa bisa yadda wasu al’umomi a jihar suka koma amfani da tukunyar gas na LPG a injunan samar da wuta da kuma ababen hawarsu maimakon gas din CNG.

Yayin wani taron manema labarai da ya gudanar jiya Lahadi 6 ga wata, jami’in yada labarai na hukumar Saminu Yusuf Abdullahi, ya ce hukumar ta lura cewa tun bayan karin farashin man fetur, mutane suka koma amfani da gas na girki a ababen hawa wanda hakan hatsarin babba.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

Jami’in yada labaran hukumar kashe gobarar ta jihar Kano ya ce, an samar da iskar gas na LPG hususan domin girki amma ba domin amfani da shi a ababen hawa ba ko kuma injunan samar da wuta na generato. 

Alhaji Saminu Yusuf Abdullahi ya ci gaba da cewa, sakamakon bincike na hukumar ya nuna cewa, kaso 4 na masu sana’o’i na amfani da tukunyar gas na LPG a injunansu na wuta, sai kaso 2.1 a gidaje yayin da kaso 1 na masu baburan haya masu kafafuwa uku sun juya amfani da kananan tukwanen gas na LPG a baburansu.

“Ina kara jan hankali ga masu amfani da tukunyar iskar gas na girki a jikin ababen hawa da kuma na’urar generator, muna shawartar masu ababen hawa da su nemi tukunyar iskar gas ta CNG don kaucewa faruwar tashin gobara a sanadiyar amfani da waccan da ba ta kamata ba.”

A game da kididdigar bala’o’in gobara da aka smau a jihar Kano kuwa a watan jiya na Yuli, jami’in yada labaran hukumar kashe gobarar ta jihar Kano ya ce, kaddarori na kusan Naira miliyan 14,350 ne suka salwanta sakamakon gobara a watan jiya, yayin da kuma ma’aikatan hukumar suka samu damar kare kayayyaki na kusan naira miliyan 31 daga barazanar gobara, sai mutum uku da suka mutu a sanadiyar gobara a jihar. (Garba Abdullahi Bagwai)