logo

HAUSA

Sudan na fuskantar hadarin yaduwar cututtuka sakamakon yake-yake a lokacin damina

2023-08-07 10:50:13 CMG Hausa

 

An yi kwanaki da dama a jare ana ruwan sama kamar da bakin kwarya a birnin Khartoum, hedkwatar kasar Sudan a watan Agusta, lamarin da ya alamta shigar lokacin damina a bana, kuma hadarin yaduwar cututtuka da dama ya karu. Bayan barkewar rikici a Sudan, biranen Khartoum da arewacin Khartoum da Omdurman sun kasance daya daga cikin yankunan da aka fi fama da rikici, tsarin kula da al’umma ya durkushe, an dakatar da dibar shara da tsabtace tituna, wadannan birane sun cika da shara makil.

A cewar MDD, sama da kashi 80 cikin 100 na asibitoci a Sudan, sun daina aiki. A birnin Omdurman mai yawan jama’a fiye da miliyan 1, asibiti daya ne kawai ke aiki yanzu, wato asibitin Alnou, shi kuma yana fama da matsalar katsewar ruwa har ma da wutar lantarki, da rashin isassun ma’aikatan lafiya da magunguna. Ban da haka kuma, an rufe kantunan sayar da magani masu yawa saboda yanayin tsaro ya yi muni, kana babu isassun magunguna.

Kwanan baya, hukumar lafiya ta kasa da kasa wato WHO ta ce, an samu barkewar cutar kyanda da kwalara a wasu sassan Sudan, inda sama da mutane dubu 2 suka kamu da cutar kyanda kana 30 kuma suka mutu sanadiyar cutar. (Tasallah Yuan)