logo

HAUSA

Mali da Burkina Faso za su aike da tawaga zuwa Nijar kan rikicin juyin mulki

2023-08-07 21:47:22 CMG Hausa

Kasashen Mali da Burkina Faso za su aike da wata hadaddiyar tawaga zuwa Yamai, babban birnin Jamhuriyar Nijar a yau Litinin 7 ga wata, a wani mataki na nuna hadin kai game da rikicin juyin mulki, in ji bangaren sojojin Mali.

Gwamnatocin rikon kwarya na Burkina Faso da Mali, wadanda aka kafa bayan da sojoji suka karbe mulki a shekarar 2020 da 2022 a kasashen biyu, sun kuma bayyana goyon bayansu ga sojojin Nijar da suka hambarar da gwamnatin Mohamed Bazoum tare da yin watsi da "takunkuman da aka kakabawa jama'ar Nijar da hukumomin kasar."

Kazalika kasashen biyu sun yi gargadin cewa, idan an dauki duk wani matakin soja a Nijar, za su mayar da shi a matsayin shelanta yaki da su, kuma hakan zai sa kasashen Burkina Faso da Mali su fice daga kungiyar tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka. (Yahaya)