logo

HAUSA

An kaddamar da cibiyar adana bayanan alkaluman kiwon lafiya a jihar Gombe

2023-08-06 21:05:44 CRI

Ma’aikatar lafiya ta jihar Gombe dake arewa maso gabashin Najeriya ta kaddamar da kwamatin masu ruwa da tsaki da zai lura da ayyukan sabuwar cibiyar tattara bayanai a game da aikace-aikacen da ake gudanarwa a fannin kiwon lafiya da sauran bangarorin gwamnati a jihar.

A lokacin da yake kaddamar da ’yan kwamitin, babban sakatare a ma’aikatar lafiya ta jihar Gombe Alhaji Danladi Adamu ya ce, cibiyar za ta taimakawa gwamnatin jihar wajen bunkasa harkokin kiwon lafiya ta hanyar sanin hakikanin alkaluma da gwamnati za ta rinka dogara da su a tsare-tsarenta.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

[!--begin:htmlVideoCode--]bc446ad71c204939a7045db1f247645a,2,1,,news[!--end:htmlVideoCode--]