logo

HAUSA

Sudan ta nada sabon ministan harkokin cikin gida

2023-08-06 15:34:45 CMG Hausa

A jiya Asabar ne shugaban majalisar rikon kwaryar kasar Sudan Abdel Fattah Al-Burhan ya nada shugaban 'yan sanda Khaled Hassan Mouheiddine a matsayin ministan harkokin cikin gida na kasar.

“Al-Burhan ya baiwa Darakta Janar na rundunar ‘yan sandan kasar Khaled Hassan ayyuka da kuma ikon ministan harkokin cikin gida,” in ji majalisar kasar a cikin wata sanarwa.

A watan Mayu ne Al-Burhan ya kori tsohon ministan cikin gida Anan Hamed Mohammed Omar, wanda shi ma ya taba aiki a matsayin babban daraktan 'yan sanda.

Tun daga ranar 15 ga watan Afrilun da ya gabata ne kasar Sudan ke fuskantar kazamin rikici tsakanin sojojin kasar Sudan da dakarun sa kai na RSF a birnin Khartoum da ma wasu yankuna, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane sama da 3,000 tare da jikkata sama da 6,000, a cewar alkaluman da ma'aikatar lafiya ta Sudan ta fitar. (Yahaya)