logo

HAUSA

Hukumar NEMA da gwamnatin jihar Kano a tarayyar Najeriya sun kaddamar da matakan saukaka annobar muhalli

2023-08-05 16:43:10 CMG Hausa

Hukumar bada agajin gaggawa a tarayyar Najeriya NEMA tare da hadin gwiwa da gwamnatin jihar Kano sun samar da wani shiri da zai taimaka wajen kyautata hanyoyin riga-kafin bala’o’in dake shafar muhalli domin dorewar cigaban zamantakewa da na tattalin arzikin jihar.

Darakta janar na hukumar ta NEMA Alhaji Mustafa Ahmed Habib ne ya tabbatar da hakan a jihar Kano dake arewacin Nijeriya yayin kaddamar da Shirin mai taken “Rage radadin bala’o’in muhalli da fadakarwa kan hanzartar shirye shiryen kare kai daga ambaliyar ruwa a damunar bana.

Daga tarayyar Najeriya wakili mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

Alhaji Mustafa Ahmed Habib yace hukumar lura da yanayi ta Najeriya NIMET da hukumar kula da zubar ruwan sama sun fitar da hasashen yanayi na shekara ta 2023, inda rahoton ya nuna cewa a bana za a samu mamakon ruwan sama kuma akwai alamu dake nuna cewa za a iya fuskantar ambaliyar ruwa sosai. 

Ya ce bisa la`akari da wannan rahoto ne ya sanya hukumar ta NEMA bazama zuwa jahohin kasar domin ganawa da masu ruwa da tsaki tun daga matakan kananan hukumomi zuwa jiha don tattauna matakan kariya da rage radadi daga irin asarorin da zasu biyo bayan wannan annoba. 

“Ina da kyakkyawan yakinin cewa kirkirar kananan ofisoshin hukumar bada agajin gaggawa mallakin jihar Kano SEMA a kananan hukumomin jihar 44 zai baiwa hukumar ta NEMA kwarin gwiwar yin aiki tare da su cikin natsuwa, kuma hakan zai samar da saukin isar da sakonni cikin gaggawa ga mazauna karkara game da kandagarkin bala’o’in ambaliyar ruwa, haka kuma wannan alaka zata taimaka sosai wajen kare tsarin samar da wadataccen abinci a kasa tare da bunkasa cigaban tattalin arzikin al`ummar jihar kano dama kasa baki daya” 

A nasa jawabin gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf wanda ya samu wakilcin sakataren gwamnatin jihar Dr. Baffa Bichi.

“Gwamnatin Kano tare da hadin gwiwa da hukumomin gwamnatin tarayyar muna shirya tarukan karawa juna sani akan ingantattun dabarun yaki da annobar ambaliyar ruwa kuma muna shirya tsarin bada gudummowa ta musamman ga masu karamin karfi dake zaune a wuraren da suke gefen kogi inda muke sake tsugunar da su a wurare masu aminci  da suke akan tudu” 

Kananan hukumomi 23 ne daga cikin kananan hukumomi 44 na jihar Kano hukumar lura da yanayi ta tarayyar Najeriya ta yi hasashen za su fuskanci matsalar ambaliyar a bana.(Garba Abdullahi Bagwai)