logo

HAUSA

Nijeriya ta rufe iyakokinta da Nijer

2023-08-05 20:21:02 CMG Hausa

Gwamnatin Nijeriya ta sanar da matakin rufe iyakokinta da jamhuriyar Nijer, saboda juyin mulkin da aka yi a kasar.

Mukaddashin shugaban hukumar kwastam ta kasar Adewale Adeniyi ne ya bayyana haka a jiya Juma’a, inda ya ce an yanke shawarar rufe dukkan iyakokin kasa dake tsakanin kasashen ne domin biyayya ga umarnin kungiyar ECOWAS na dakatar da jigilar kayayyaki har sai baba-ta-gani.

Adewale Adeniyi ya bayyana haka ne yayin ziyarar da ya kai garin Jibia na jihar Katsina dake arewacin kasar, wanda ke kan iyakar Nijeriya da Nijer. Ya kuma kara da cewa, an dauki matakin ne domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali tsakanin kasashen biyu. (Fa’iza Mustapha)