logo

HAUSA

Kungiyoyin fararen hulla na ci gaba da kawo goyon baya ga sabbin hukumomin kasar Nijar

2023-08-05 18:15:59 CMG Hausa

Tun bayan juyin mulkin da ya wuce da shugaba Mohamed Bazoum a ranar 26 ga watan Yulin da ya gabata, kwamitin kiyayewa da ceton kasa CNSP na sojojin da suka karbe iko a karkashin jagorancin birgadiye janar Abdourahamane Tchiani na cigaba da samun goyon baya daga bangarori daban daban na al’ummar kasa.

Daga birnin Yamai abokin aikinmu Mamane Ada ya aiko mana da wannan rahoto :

Tun bayan da kungiyar CEDEAO ko ECOWAS, ta bayyana niyyarta ta maido da tsarin mulkin demokuradiyya da shugaba Mohamed Bazoum kan karagar mulki ta kowane hali, musamman ma ta hanyar matakan soja, idan hanyar sulhu ba ta yi nasara ba. Idan hakan ya faru a cewar shugabannin ECOWAS babu wata hanyar sulhuta wannan rikicin kasar Nijar illa ta matakan soja. Bisa ga wannan niyya ta gamayyar yammacin Afrika, kwamitin soja na CNSP bai jira ba domin bayyana cewa kasar Nijar a shirye take wajen maida martani kan dukkan wani matakin soja na ECOWAS a cikin kasarta. Wannan mataki da sojojin suka dauka ya samu goyon bayan bangarori daban daban na al’ummar Nijar ta hanyar gudanar da tarukan gangami da zanga zanga a birnin Yamai da sauran yankuna domin yin allawadai da kungiyar ECOWAS da sauran kasashen yammacin duniya musammun ma kasar Faransa. A daya bangare kuma kowace rana, kungiyoyin fararen hula na mataki daban daban suna ci gaba da fitowa ta hanyar gidan rediyo da talabijin domin shaida ma duniya cewa al’ummar Nijar mafi rinjaye na goyon bayan juyin mulkin da ya hambarar da shugaba Mohamed Bazoum. 

Mamane Ada, sashen hausa na CRI daga Yamai a jamhuriyar Nijar