logo

HAUSA

Manyan hafsoshin tsaron ECOWAS sun bayyana tattaunawa a matsayin wata hanya ta shawo kan rikicin Niger

2023-08-05 15:52:41 CMG Hausa

 

Manyan hafsoshin tsaron kasashe mambobin kungiyar raya tattalin arzikin yammacin Afrika (ECOWAS), sun ce ya kamata a samu hadaddun dabarun shawo kan yanayin Niger, kuma kamata ya yi tattaunawa da yarjejeniyoyi su kasance a kan gaba.

Kwamitin hafsohin tsaro na kungiyar ECOWAS ya bayyana haka ne a karshen taron kwanaki 3 da ya yi a Abuja, babban birnin Nijeriya.

Wata sanarwar hadin gwiwa da manyan hafsoshin tsaron kasashe mambobin kungiyar ECOWAS din suka fitar a jiya Juma’a, ta ce kwamitin ya nazarci tasirin juyin mulkin Niger da yadda zai iya shafar fadin yankin yammacin Afrika baki daya, da kuma nazarin yanayin Niger da bukatar gaggawa ta samar da ingantaccen martani. (Fa’iza Mustapha)