logo

HAUSA

Jagoran juyin mulki a Nijar ya yi watsi da takunkuman ECOWAS

2023-08-04 11:37:11 CMG Hausa

Shugaban majalissar tsaron kasa a jamhuriyar Nijar Abdourahamane Tchiani, wanda kuma ke rike da jagorancin kasar tun bayan juyin mulkin soji da ya wakana a makon jiya, ya ce ba su amince da takunkuman da kungiyar raya tattalin arzikin yammacin Afirka ta ECOWAS, da kungiyar kasashe masu amfani da kudin Sefa a yammacin Afirka ko UEMOA suka kakabawa kasar ba. Abdourahamane Tchiani ya bayyana hakan ne a daren ranar Laraba.

Kafin hakan, yayin taron jagororin ECOWAS da UEMOA, wanda ya gudana a ranar Lahadin karshen makon jiya a birnin Abuja, fadar mulkin Najeriya, an amince da kakabawa sojojin juyin mulki a Nijar takunkumai. Kaza lika shugabannin kungiyoyin biyu, sun baiwa sojojin wa’adin mako guda, da su mayar da amfani da kundin tsarin kasar, tare da gargadinsu da cewa, za su iya fuskantar matakan soji, idan har suka ki amincewa da umarnin.

A jiya Alhamis ne kuma, sojin dake rike da iko a Nijar suka ayyana jingine yarjejeniyoyin hadin gwiwa na aikin soji tsakanin kasar da Faransa, biyowa bayan tunbuke gwamnatin farar hula ta Mohamed Bazoum. Kaza lika sojojin sun ayyana kawo karshen ayyukan jakadun Nijar a kasashen Faransa, da Najeriya da Togo da kuma Amurka. 

Faransa dai na da dakarun soji tsakanin 1,000 zuwa 1,500 a jamhuriyar Nijar, wadanda ke taimakawa kasar wajen yaki da dakarun al-Qaeda da IS, wadanda ke kaddamar da hare-hare a sassan yankin. (Saminu Alhassan)