logo

HAUSA

Najeriya ta musanta hada runduna domin daukar matakin soji a Nijar

2023-08-04 11:35:10 CMG Hausa

Rundunar sojin Najeriya ta yi watsi da rahotannin da wasu kafafen yada labarai ke yadawa a baya-bayan nan cewa, tana shirin hada dakarunta domin daukar matakin soji kan gwamnatin mulkin soja a Nijar.

Rundunar sojin kasar dai ba ta samu umarnin shiga tsakani a Nijar bayan juyin mulkin ba, kamar yadda wata sanarwa da Tukur Gusau, kakakin rundunar sojin ya fitar a ranar Laraba ya bayyana.

Sanarwar ta ce, kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka ECOWAS na da zabubbuka daban-daban dangane da martini ga mamayar gwamnati ba bisa ka'ida ba da wasu shugabannin sojoji suka yi a Nijar, kuma zabin karfin soja shi ne "zabi na karshe" idan sauran zabubbukan suka gaza daidaita lamarin.

A daya bangaren kuma, a wani taron manema labarai da aka gudanar a Dakar, babban birnin kasar Senegal a ranar 3 ga wata, ministan harkokin wajen kasar Senegal Aissata Tall SALL, ta bayyana cewa, idan kungiyar ECOWAS, ta dauki matakin soja kan kasar Nijar don shiga tsakani, to kasar Senegal ba za a bar ta a baya ba. (Yahaya Babs)