logo

HAUSA

Shugabannin mulkin soji a Niger sun dakatar da kafafen yada labarai na Faransa

2023-08-04 19:54:00 CMG Hausa

 

Shugabannin soji da suka yi juyin mulki a Jamhuriyar Niger, sun dakatar da kafafen yada labarai na kasa da kasa mallakin kasar Faransa da suka hada da France 24 da RFI, lamarin da ma’aikatar harkokin wajen Faransar ta yi tir da shi.

Da farko a jiya Alhamis, daruruwan masu zanga-zanga ne suka yi tattaki a birnin Yamai domin nuna adawarsu da matsin lambar da kasashen waje ke yi wa shugabannin sojin. Baya ga takunkumai, kungiyar ECOWAS ta yankin, ta ce za ta bayar da umarnin amfani da karfin soji idan aka gaza mayar da Mohamed Bazoum kan karagar mulki zuwa ranar Lahadi.

Shugabannin mulkin sojin, sun dage dokar takaita zirga-zirga da suka sanya bayan juyin mulkin da hambarar da zababben shugaban kasar, a ranar 26 ga watan Yuli. (Fa’iza Mustapha)