logo

HAUSA

Mutane 79,000 ne suka rasa rayukansu a Najeriya sakamakon cutar Daji a duk shekara

2023-08-04 09:10:35 CMG Hausa

Gwamnatin tarayyar Najeriya tare da hadin gwiwa da kungiyoyi agajin kiwon lafiya na kasa da kasa za su hada hannu wajen dakile karuwar matsalolin cutar daji a tsakanin al’umma inda a duk shekara take sanadin mutuwar mutane 79,000 a kasar.

Babban-sakatare a ma’aikatar lafiya ta tarayyar Najeriya Injiniya Funso Adebiyi ne ya tabbatar da hakan a birnin Abuja yayin taron sanya hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna da aka kulla domin yaki da cutar.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto. 

Kamar dai yadda yake kunshe cikin sanarwar da babban-sakataren ya fitar, hukumomi da kungiyoyin da suka kulla wannan alaka dai sun hada da ma’aikatar lafiya ta tarayyar Najeriya da hukumar raya birnin Abuja, da cibiyar lafiya ta Clinton da kuma gidauniyar yaki da ciwon daji ta Medicaid.

Babban-sakataren ya tabbatar da cewa samun hadin kan wadannan hukumomi da cibiyoyin lafiya masu zaman kansu zai taimaka sosai wajen kara karfafa kokarin ma’aikatar lafiya ta tarayyar Najeriya na samar da al’umma mai cike da koshin lafiya tare kuma da rage mace-macen da ake samu sakamakon ciwon na daji.

Ya ce, Najeriya ita ce kasa ta biyu na yawan masu kamuwa da cutar daji a nahiyar Afrika, inda a duk shekara ana samun mutum dubu 124 da suke kamuwa da ita wannan cuta.

Dr Saminu Muhammad babban likita ne a sashen masu lura da cutar kansar na asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano, ya ce hakika ana fama da matsalolin cutar kansar wanda kuma ake kira da ciwon daji a tarayyar Najeriya duk da cewa kansar ta rabu gida da yawa.

“Akwai kansa ta Nono, akwai ta Jini, akwai ta huhu, akwai ta hanji babban da karami, akwai kansa ta bakin mahaifa, amma a Najeriya kansar da ta fi shafar mutanenmu ita ce kansar mama wadda ta fi samun mata da yawa, kuma kwarai kamar yadda aka ba da rahoto cewa ana samun cases ko matsaloli na kansa suna karuwa haka ne, fiye da kaso 50 na abubuwan da suke kawo kansar gaskiya yawanci canjin abinci ne sannan sai abubuwa da ake gada na halitta. Gwamnatoci da mu likitoci muna kokari wajen ganin mun dakile karuwar wannan cuta ta kansa a wannan kasa ta hanyar fadakar da mutane cimaka mai kyau da kuma yadda za su je asibiti a kan lokaci domin a san abun da za a yi idan sun kamu da kansa, idan kuma a matakin da za a iya kare mutum ne za a yi kokari a kare mutum kafin a ce ta shafe shi sosai.” 

Dr Saminu Mohammed ke nan babban likita a sashen kula da masu ciwon kansa dake asibitin koyarwa na malam Aminu Kano. (Garba Abdullahi Bagwai )