logo

HAUSA

Sin ta mikawa gwamnatin Sudan kashin farko na tallafin jin kai

2023-08-03 09:55:36 CMG Hausa

Ofishin jakadancin kasar Sin dake Sudan, tare da jami’an gwamnatin kasar, sun gudanar da bikin karbar kashin farko na kayayyakin tallafin jin kai da Sin ta baiwa kasar Sudan. An gudanar da bikin ne a jiya Laraba, a birnin Port Sudan na gabar ruwa.

Kayayyakin da kasar ta Sin ta baiwa Sudan tallafinsu a wannan karo, sun kai kusan tan 4.6, sun kuma kunshi kayayyakin jinya, da na kiwon lafiya, da magunguna da sauransu. 

Rahotanni na cewa, Sin za ta ci gaba da aikewa da tallafi a kai a kai ga kasar ta Sudan, tsakanin watan Agustan nan zuwa Satumba.

Wani rahoto da ofishin MDD mai lura da ayyukan jin kai ya fitar, ya nuna cewa, tsakanin watan Yuli zuwa Satumba dake tafe, kimanin al’ummar Sudan miliyan 20.3, wato kaso kusan 42 bisa dari na daukacin al’ummar kasar, za su fuskanci barazanar karancin abinci.(Saminu Alhassan)