logo

HAUSA

Shugabannin tsaron ECOWAS sun gana kan juyin mulkin da aka yi a Nijar

2023-08-03 10:07:17 CMG Hausa

A jiya ne, manyan hafsoshin tsaron kasashen kungiyar ECOWAS mai mambobi 15, suka fara wani taro na kwanaki 3 a Najeriya, kan halin da ake ciki a jamhuriyar Nijar.

Babban hafsan tsaron Najeriya Christopher Musa, wanda ke shugabantar kwamitin hafsan hafsoshin tsaron kungiyar ta ECOWAS, ya shaidawa manema labarai a yayin bude taron cewa, shawarar da za a yanke, za ta yi tasiri matuka ga yankin na ECOWAS, inda ya yi kira da a hada kai, domin daukar mataki na bai daya, wajen ganin an dawo da mulkin demokradiyya a jamhuriyar Nijar.

Babban hafsan tsaron Najeriyar, ya bukaci takwarorinsa da su hada kai don aikewa da sako mai karfi game da jajircewar demokuradiyya, da rashin amincewa da sauye-sauyen gwamnati da ya saba doka, da sadaukar da kai ga wanzar da zaman lafiyar yankin.

Wata majiya a wajen taron ta shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, manyan hafsoshin tsaro daga kasashen Mali, da Nijar, da Guinea, da Burkina Faso, da Guinea-Bissau ba su halarci taron ba. (Ibrahim)