logo

HAUSA

Gwamnatin mulkin Soja ta Nijar ta ce ba za ta ja da baya ba duk da takunkumin da aka kakaba mata

2023-08-03 09:44:42 CMG Hausa

Sabon shugaban jamhuriyar Nijar da ya ayyana kansa a ranar Larabar da ta gabata ya ce duk da matsin lambar da gwamnatin mulkin sojan kasar take sha, ba za ta dawo da hambararren shugaban kasar Mohamed Bazoum kan mulki ba, lamarin da ke kara tsananta takun saka tsakaninsa da kungiyar  kasashen yammacin Afirka da ke kokarin shiga tsakani bayan juyin mulkin da aka yi a makon jiya.

Kungiyar tarayyar tattalin arzikin yammacin Afirka ta kakabawa Nijar takunkumi, inda ta ce za ta iya ba da izinin yin amfani da karfin soja idan masu juyin mulkin ba su maido da shugabancin Bazoum cikin mako guda daga ranar Lahadin da ta gabata ba.

Wutar lantarki da Najeriya ke samar wa Nijar kan layin wutar lantarki mai karfin MegaWatt 80 a birnin Kebbi ya yi kasa zuwa sifili a ranar Laraba, kamar yadda takardar aikin samar da wutar lantarkin kasa Nijar ta nuna.

Kungiyar ECOWAS mai kasashe 15 da ta hada da Najeriya ta yanke shawarar rufe iyakokinta da Nijar a ranar Lahadin da ta gabata, da hana zirga-zirgar jiragen sama na kasuwanci da kuma dakatar da hada-hadar kudi bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a makon jiya.

A gefe guda kuma, a ranar Larabar da ta gabata ne Amurka ta ba da umarnin kwashe wani bangare na ma’aikatan ofishin jakadancinta a Nijar, kamar yadda ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta bayyana. (Yahaya)