logo

HAUSA

Shugaban tarayyar Najeriya ya gana da shugabannin kodago kasar inda ya bukaci su kara ba shi lokaci kadan

2023-08-03 09:16:54 CMG Hausa

Da yammacin jiya Laraba ne shugaban tarayyar Njaeriya Bola Ahmad Tinubu ya yi wata kwarya-kwaryar ganawa da shugabanin kodagon kasar a fadar sa dake Abuja inda ya bukaci da a kara ba shi lokaci, bada jimawa ba za a  warware matsalolin da ma’aikata da sauran al’ummar kasa ke fuskanta.

Shugaban ya ce, yajin aiki ko zanga-zanga ba shi da amfani ko kadan a daidai lokacin da ake fafutukar saita al’amuran a kasar.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

Ganawar dai ba ta dauki wani lokaci mai tsawo ba saboda taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar mai mulki da aka gudanar jiya wanda kuma shugaban shi ne jagoran taron.

A dan takaitaccen sanarwar da shugaban kungiyar kodagon na tarayyar Najeriya Mr Joe Ajaero ya bayar jim kadan da kammala taron ya ce, bukatar na shugaban kasa yana tafiya ne tare da irin bayanai da mai tsawatarwa majalissar dattawa Sen Ali Ndume ya yi musu lokacin da suka jagoranci zanga-zanga zuwa harabar majalissar dattawan a jiya Laraba.

Shugabanni a kan bukatar shugaba Tinubu a taron da za su gudanar yau din nan Alhamis, inda a nan ne za su yanke shawara ta karshe. 

Kafin zuwan shugabanin kungiyar kodagon zuwa fadar shugaban kasa, sai dai suka jagoranci dandazon kungiyoyin ma’aikata zuwa harabar majalissar dokoki ta kasa, kuma  Sen Ali Ndume ne ya tarbe su a madadin shugaban majalissar, inda ya yi kira ga shugabannin kungiyoyi kodagon da su dakatar da zanga-zangar gama-garin, su baiwa majalissar dattawar mako guda domin yin wani abu a kan bukatunsu.

Sanata Ali Ndume ya yi wa manema labarai karin haske a game da kalaman da ya yi wa ’yan kodagon yayin wannan zanga-zanga.

“Abun da suke yi daidai  ne don kowanne talaka a Najeriya ya san irin radadin da aka shiga ciki don janye tallafin mai da aka yi, kuma matakan da aka ce za a dauka ba a gansu a kasa ba, to mun ce su yi hakuri don ba abu ne na kwana daya ba, kuma mu majalissar dattawa ranar Litinin da ta gabata ganin cewa, tattaunawar da suke yi da gwamnati ya samu matsala ko kuma ya tsaya, muka ce mu a matsayin wakilan jama’a, ya kamata mu shiga cikin lamarin mu ga yadda za mu sassanta tsakanin ’yan kodagon, kuma alhamdulillahi mun samu hadin kai daga wajensu, kuma mun ba su kwana takwas a kan cewa za mu fara wannan tattaunawa tsakaninsu. Mu kamar mun zama masu shiga tsakani ne mediator don mu tabbatar cewa, an samu masalaha a kan yaya za a yi da wannan matsala na cire tallafi.”

Daga cikin bukatun ’ya’yan kungiyar Kodagon dai sun hada da neman gwamnati ta dawo da farashin mai zuwa 520 maimakon 617, haka kuma kungiyar ta yi kira ga gwamnatin da ta gyara matatun mai domin dai a daina odar mai daga waje. (Garba Abdullahi Bagwai)