logo

HAUSA

Manzon MDD: Rikicin Nijar na iya dagula yanayin tsaro a yammacin Afirka

2023-08-02 09:42:26 CMG Hausa

Wakilin babban sakataren MDD na musamman a yammacin Afirka da Sahel, Leonardo Santos Simao ya bayyana cewa, yanayin tsaro a yammacin Afirka zai iya tabarbare, idan har ba a magance rikicin Jamhuriyar Nijar ba.

Jami’in ya shaidawa manema labarai hakan ne, a hedkwatar MDD dake birnin New York ta kafar bidiyo daga birnin Accra na kasar Ghana.

Bugu da kari, wakilin babban sakataren, kana jagoran ofishin MDD mai kula da yammacin Afirka da yankin Sahel ya ce, rikicin zai yi mummunan tasiri ga ci gaba da rayuwar jama'a a kasar da mutane miliyan 4.3 ke bukatar agajin jin kai.

A bangare guda kuma, babban sakataren MDD Antonio Guterres ya bayyana matukar damuwarsa kan rahotannin kama wasu jami’an gwamnatin Nijar.

Mataimakin kakakin babban sakataren MDD Farhan Haq, ya shaidawa manema labarai cewa, ko da a jiya ma Guterres ya yi kira da a martaba dokokin kiyaye hakkin dan Adam na kasa da kasa a Nijar, da kuma gaggauta maido da odar kundin tsarin mulkin kasar. (Ibrahim)