logo

HAUSA

Shugaban Najeriya ya yi kira da a kwantar da hankula yayin da ake jin radadin tsauraran manufofin tattalin arziki

2023-08-02 10:19:28 CMG Hausa

A cikin jawabinsa da ya gabatar wa al’ummar kasa a daren Litinin, Shugaban Najeriya Bola Ahmad Tinubu ya yi kira da a kwantar da hankali da hadin kai yayin da ake mayar da martani ga aiwatar da tsauraran manufofi na baya-bayan nan wadanda ke nufin daidaita tattalin arzikin kasar. 

A baya-bayan nan ne gwamnatin Najeriya ta kaddamar da gagarumin sauye-sauye a fannin tattalin arziki da aka tsara domin dakile hauhawar farashin kayayyaki, da daidaita farashin kudaden kasar waje domin magance hawa da saukar kudaden kasar ke fuskanta in aka kwatanta da manyan kudaden duniya, da cire tallafin man fetur, da magance gibin kasafin kudi, da inganta kudaden shiga. Matakan da gwamnatin ta dauka sun kuma hada da yin gyare-gyare a fannin haraji, da karfafa gwiwar zuba jari don zaburar da masana'antun cikin gida da jawo jarin waje kai tsaye, da farfado da fannin noma da masana'antu, wadanda ke da damar samar da ayyukan yi da bunkasar tattalin arziki mai dorewa.

Tinubu ya kara da cewa gwamnati za ta tabbatar da samar da abinci mai gina jiki da kuma araha ga ’yan kasa cikin kankanin lokaci a matsayin hanyoyin dakile illolin tsadar rayuwa. (Yahaya Babs)