logo

HAUSA

Shugabannin kwamitin tsaro na kungiyar ECOWAS za su gana domin tattauna halin da ake ciki a Nijar

2023-08-02 14:01:21 CMG Hausa

A jiya 1 ga watan Agusta, shafin yanar gizo na kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka ECOWAS, ya bayyana cewa, shugabannin kwamitin tsaro na kungiyar ta ECOWAS za su gudanar da wani taro a birnin Abuja na Najeriya daga yau 2 zuwa 4 ga watan Agusta domin tattauna halin da ake ciki a Jamhuriyar Nijar.

A wani taron koli na musamman da aka gudanar a ranar 30 ga watan Yuli, kungiyar ta kasashen yammacin Afirka ta bayyana cewa, idan sojojin Nijar suka gaza mika mulki cikin kwanaki 7, kungiyar za ta dauki dukkan matakan da suka dace, ciki har da yin amfani da karfin soja wajen maido da tsarin mulkin kasar. Shugabannin kwamitin tsaro na ECOWAS na iya gudanar da wani taro don tattaunawa kan takamaiman bayanai da tsare-tsare na yin amfani da karfin soja. (Yahaya Babs)