logo

HAUSA

An kaddamar da shirin sayar da kayan aikin gona ga manoma a jihar kano

2023-08-02 10:15:17 CMG Hausa

 

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta kaddamar da shirinta na  sayar da kayan aikin gona ga manoman dake wasu jihohin arewacin  kasar kan farashi mai sauki a jihar Kano.

A lokacin da yake kaddamar da shirin a karamar hukumar Bunkure, babban sakataren ma’aikatar aikin gona da raya karkara na tarayyar Dr Ernest Afolabi ya ce, manoman da suka fito daga jihohin Jigawa, Kebbi, Niger da kuma Sakkwato ne za su ci gajiyar shirin, inda za su amfana da takin zamani da maganin feshi da kuma ingantaccen irin shuka.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

Babban sakataren wanda ya samu wakilcin daraktan tsare-tsaren manufofi na ma’aikatar Malam Tanimu Ibrahim ya ce, fara sayar da kayan da aka yi a jihar Kano ya nuna kankamar shirin samar da kayan aikin gona na shekara ta 2023 wanda kuma aka kiyasta cewa a kalla manoma dubu 60 za su amfana a jihohi 5 dake arewacin Najeriya. 

Ya ce an kirkiro da shirin ne bisa tallafin bankin raya kasashen Afrika tun a watan Maris na 2015 da nufin bunkasa sha’anin samar da wadataccen abinci a kasa, tare kuma da jan hankalin bangarorin masu zaman kansu wajen saka jarinsu a bangaren noma da cinikin kayan amfani gona da kuma samar da kayan aikin noma.

“Domin tabbatar da gaskiya da adalci wajen rabar da kayayyakin, gwamnati ta amince da gabatar da tsarin amfani da wata manhajar sadarwar zamani inda za a rinka aiko wa manoma da suka samu dacewa da amfana da hotunan kayayyakin da aka ba su da kuma wuraren da za su je su dauki kayan ta hanyar wayoyinsu na salula, wanda wannan ya sanya shirin na bana ya bambanta da na lokutan baya.”

Malam Tanimu Ibrahim ya bayyana cewa gwamnati ce za ta biya kaso 80 na adadin kudin farashin kayan da aka bayar yayin da kuma manomi kuma zai biya kaso 20 kacal.

Da yake nasa jawabin, mataimakin gwamna na jihar Kano kuma ya yi kira ga manoman da suka amfana da shirin da su kaucewa sayar da kayan da aka ba su.

“Wanda duk ya samu kansa a cikin wannan shiri ya godewa Allah ya zage damtse ya yi amfani da abun da aka ba shi don cin moriyar wannan tsari wannan tallafi da wasu bayin Allah suka zauna suka tsara don ci gabanmu don bunkasar tattalin arzikinmu, don wadatar abinci a cikin kasarmu.”

Manoman za su biya kudin kayan ne bayan kammala girbin amfanin gonarsu. (Garba Abdullahi Bagwai)