logo

HAUSA

Za a kaddamar da tashar wutar lantarki da Sin ta fadada a Zimbabwe

2023-08-01 09:59:41 CMG Hausa

Ministan makamashi da raya wutar lantarki na kasar Zimbabwe Soda Zhemu ya bayyana a jiya Litinin cewa, yawan dauke-dauke na wutar lantarki ya zama tarihi a kasar Zimbabwe bayan kammala aikin fadada tashar wutar lantarki na Hwange sashe na 7 da na 8.

Kamfanin Sinohydro na kasar Sin ya gudanar da aikin, inda ya kara karfin megawatt 600 ga tashar samar da wutar lantarki ta Hwange, babbar tashar samar da wutar lantarki ta kasar.

Shugaban kasar Emmerson Mnangagwa ne zai kaddamar da aikin a ranar Alhamis.

Zhemu ya bayyana a wani taron manema labarai cewa, rahotannin da kafafen yada labarai na baya-bayan nan suka bayar na hasashen ci gaba da dauke wutar lantarki bayan watan Agusta karya ne, domin a yanzu akwai tabbacin samar da tsayayyen wutan lantarki a Zimbabwe na watadaccen lokaci. (Yahaya)