logo

HAUSA

Shugaban AU ya bukaci a kawo karshen sauye-sauyen gwamnati ba bisa ka'ida ba a Afirka

2023-08-01 09:32:04 CMG Hausa

Shugaban hukumar gudanarwar kungiyar tarayyar Afirka (AU) Moussa Faki Mahamat, ya yi tir da yadda a baya-bayan nan ake samun sauye-sauyen gwamnati da ya sabawa tsarin mulkin Afirka.

Shugaban hukumar ta AU ya yi tir da hakan ne, a yayin wani taron gaggawa da kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka ta ECOWAS ta gudanar ranar Lahadin da ta gabata, kan halin da ake ciki a Jamhuriyar Nijar.

Da yake tir da juyin mulkin na baya-bayan nan da aka yi a Nijar, Faki ya ce lamarin ba Nijar kadai zai iya shafa ba, domin zai yi tasiri a yankin baki daya.

Faki ya ce, yanayi na rashin hankali game da wannan juyin mulki, da yadda aka take ka'idojin kungiyar ta AU da kuma babbar barazana da zai iya haifarwa ga zaman lafiyar kasashen yankin, na nufin dole ne a yanke shi. Yana mai cewa, wannan juyin mulkin, kamar dukkan sauye-sauyen gwamnatoci ba bisa ka'ida ba ta hanyar da sojoji suka dora kan su a kan mulki, dole ne a kawo karshensa baki daya.

Faki ya yi gargadin cewa, rashin dakatar da juyin mulki a Afirka, na iya zama wata hanya ta samun yawaitar irin wadannan sauye-sauyen gwamnatoci da suka saba wa kundin tsarin mulkin kasashen nahiyar. (Ibrahim)