logo

HAUSA

Bayan watanni biyu da janye tallafin mai, gwamnatin tarayyar Najeriya ta samu adana sama da naira tiriliyan 1

2023-08-01 13:14:48 CMG Hausa

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta sanar da cewa, a tsakanin watanni biyu da suka gabata ta samu damar adana tsabar kudi sama da naira tiriliyan 1.

Bayanin hakan na kunshe cikin jawabin da shugaban tarayyar ta Najeriya Bola Ahmad Tinubu ya yi wa al’ummar kasar jiya Litinin 31 ga wata, ya ce yanzu gwamnati za ta yi amfani da wani kaso na kudin wajen saka jari a fannin makamashin CNG mai aminci da rage dumanar yanayi da kuma sha’anin bunkasa kanana da matsakaitan masana’antu.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

Shugaban na tarayyar Najeriya ya ce kowa zai mamakin ganin cewa a lokutan baya wasu kalilan din mutane ke amfana da wadancan makudan kudade da gwamnati ta same su cikin watanni biyu kawai.

Shugaban na tarayyar Najeriya ya ce ba shi da niyyar zartar da duk wata manufa da zummar sanya al’ummar kasar cikin wani mawuyacin hali, a kullum burinsa shi ne bullo da tsare-tsare da za su ci gaba da sanya kwanciyar hankali da walwala a zukatan al’umma.

Ya ce, a yanzu haka gwamnati ta kammala shirye-shiryen samar da makudan kudade ga bangarori da dama domin ragewa ’yan kasa radadin tsadar rayuwa da suke cikin, tsadar rayuwar da kamar yadda fada yana daf da zama tarihi.

Shugaba Tinubu ya ce, gwamnatinsa tana daukar bangaren kanana da matsakaitan masana’antu da muhimmancin gaske wannan ce ta sanya ma.

“Za mu kara kyautata wannan muhimmin bangare da samar masa da kudi har naira biliyan 125, inda daga cikin adadin wadannan  kudade za a yi amfani da naira biliyan 50 wajen bayar da su tallafi ga masu kananan sana’o’i miliyan guda daga yanzu zuwa watan Maris na shekarar badi. Abun da muke son cimmawa shi ne a kalla mu baiwa  masu kananan sana’o’i har dubu 1,300 da za a zakulo daga kananan hukumomin tallafin naira dubu 50 kowannensu.”

A kan batun abinci kuwa, shugaba Tinubu ya ci gaba da cewa,

“Na ba da umarnin fito da abinci har ton dubu dari 2 dake ma’ajiyar daban daban domin rabawa ga magidanta a jahohi 36 har da Abuja  domin dai saukaka farashi, ha’ila yau za’a bayar da takin zamani har ton dubu 225 da irin shuka da kuma kayan aikin gona domin rabawa ga manoman da suke nuna himma wajen cimma manufar gwamnati na samar da wadataccen abinci, haka kuma gwamnati ta ware makudan kudade domin noma hekta dubu 500 a bangarori daban-daban na kasar, baya ga samar da abinci wannan shiri zai samarwa da matasa marasa aikin yi sana’o’i na wucin gadi,

“Gwamnatinmu za ta kashe naira buliya 50 domin noma hekta dubu 150 na gonakin marasa da kuma shinkafa.” (Garba Abdullahi Bagwai)