logo

HAUSA

Ci gaban rikicin Sudan ta sanya kasar tsawaita rufe sararin samaniyarta zuwa tsakiyar Agusta

2023-07-31 11:25:56 CMG Hausa

Wata sanarwar da babban filin jirgin saman Khartoum na kasar Sudan ta fitar a yau Litinin ta ce, hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta kasar ta tsawaita rufe sararin samaniyar Sudan har zuwa ranar 15 ga watan Agusta, sai dai rufewar ba ta hada da jiragen agajin jin kai da na fitar da mutane ba. 

An rufe sararin samaniyar kasar Sudan tun bayan barkewar fada a tsakiyar watan Afrilu, yayin da na’urorin zirga-zirgar jiragen sama a filin tashi da saukar jiragen saman suka samu matsala a dalilin fadace-fadace tsakanin bangarorin dake fito-na-fito da juna.

A ranar 15 ga Afrilu ne rikici ya barke tsakanin sojojin Sudan da dakarun sa kai na martanin gaggawa, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane sama da 3,000 da jikkata sama da 6,000, a cewar alkaluman da ma'aikatar lafiya ta Sudan ta fitar.

Fiye da mutane miliyan 3 ne suka rasa matsugunansu a ciki ko wajen kasar, tun bayan barkewar rikici a Sudan, a cewar alkalumman majalisar dinkin duniya. (Yahaya)