logo

HAUSA

Ecowas ta zartas da shawarar daukar tsauraran matakai 8 ga sojin Nijar

2023-07-31 09:05:02 CMG Hausa

Kungiyar raya tattalin arzikin kasashen Afrika ta yamma ECOWAS ta yi barazanar zartas da hukunci mai tsananin gaske ga sojin da suka yi juyin mulki a jamhuriyyar Nijar muddin dai suka gaza maido da shugaba Mohamed Bazoum kan kujerarsa nan da kwanaki 7 masu zuwa.

Kungiyar ta sanar da hakan ne jiya Lahadi a birnin Abuja yayin wani taron gaggawa da ta gudanar karkashin jagorancin shugaban kungiyar kuma shugaban tarayyar Najeriya Bola Ahmed Tinubu, kungiyar ta ce, matakai 8 din sun hada da rufe dukkan iyakokin kasar ta sama da ta kasa.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdulalhi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

A jawabin bayan taron da shugaban hukumar kungiyar ta ECOWAS Omar Touray ya karanta, kungiyar ta ce ita a wajenta har yanzu shugaba Mohamed Bazoum shi ne halartaccen shugaban kasar Jamhuriyar Nijar wanda aka zaba bisa doron demokradiyyar.

Taron shugabannin kungiyar kuma ya bukaci sojojin da suke tsare da shugaba Bazoum da su gaggauta sakinsa tare da mayar da shi kan matsayinsa, haka kuma kungiyar ba ta amince da duk wani nau’i na murabus ba da sojojin suke kokarin tursasa shugaba Bazoum da aiwatarwa.

Shugaban hukumar gudanarwar kungiyar ta Ecowas Mr Omar Touray ya sanar da cewa shugabannin kasashen dake cikin kungiyar sun amince da murya guda wajen daukar dukkannin matakan da suka dace domin dai maido da tsarin mulkin demokradiyya a kasar, matakan kuwa da suka hada da amfani da karfin tuwo ta hanyar aiyukan hadakar jami’an tsaron kasashen dake cikin kungiyar, sauran kuma sun hada da, “Hana zurga-zurgar jiragen sama na kasuwanci a kasar, dakatar da duk wata hulda ta kudi tsakanin kasar ta Nijar da kasashe membonin kungiyar Ecowas, dakatar da mu’amulla ta kasuwanci da ta hada ta makamashi, rike dukkannin kaddarorin kasar ta Nijar dake babban bankin kungiyar Ecowas, za mu rike kaddarorin jahohin kasar da na kananan hukumomi da kuma na kamfanoni mallakin gwamnatin kasar dake bankunan kasuwanci.”

“Sai dai dakatar da kasar daga amfana da duk wani taimakon kudi daga hukumomin hada-hadar kudade na kasa da kasa, za kuma a sanya takunkumin hana zurga-zurga da rike kudade da kaddarorin jami’an sojin da suka kitsa juyin mulkin da iyalansu da kuma duk wani farar hula da ya amince zai amshi mukami a gwamnatin da jami’an sojin suka kafa.”

Daga bisani shugaban hukumar gudanarwar kungiyar ta ECOWAS Mr. Omar Touray ya bayyana gamsuwarsa ga yadda shugaban kungiyar Bola Ahmad Tinubu ke tafiyar da harkokin kungiyar tun bayan da ya kasance jagoranta. (Garba Abdullahi Bagwai)