logo

HAUSA

Sojojin CNSP sun gana da sakatarori na hukumomin gwamnati

2023-07-31 13:38:35 CMG Hausa

A kwanan nan ne, kwamitin soja na CNSP a karkashin jagorancin birgadiye janar Abdourahamane Tchiani ya yi ganawa ta farko tare da sakatarori ma’aikatun gwamnati domin halin da ake ciki wajen tafiyar da hidimar kasa, tun bayan juyin mulkin a kasar Nijar.

Wakilinmu, Mamane Ada ya turo mana da rahoto daga birnin Yamai. 

Shugaban kwamitin soja na CNSP da ya hambarar da mulkin Mohamed Bazoum ya yi wannan ganawa ne da dukkan sakatarorin ma’aikatun gwamnati da makarrabansu a fadar shugaban kasa dake nan birnin Yamai. Birgadiye janar Abdourahamane Tchiani, shugaban kwamitin soja na CNSP tare da sauran mambobin kwamitin sun gana tare da sakatarori na ofishin ministoci da hukumomin na gwamnati. A tsawon wannan tattaunawa ta fiye da sa’o’i biyu, bangarorin biyu sun maida hankali kan batun ci gaba da hidimar kasa da kuma sanin halin kasa bisa ga yin kira ga ’yan kasa da su dukufa wajen aiki da gina kasa. A yayin wannan haduwa, kowane sakatare-janar na kowace ma’aikatar gwamnati ya gabatar da rahohto kan halin aiki da abin da suke bukata domin ci gaba da hidimar kasa. Shugaban kwamitin soja na CNSP, birgadiye-janar Tchiani ya yi kira ga wadannan sakatarori da aka dora ma wannan nauyi da kada su yi kasa a gwiwa domin tafiyar da harkokin kasa. Haka kuma, jim kadan bayan kammala wannan zaman taro na farko tun bayan kama aikin kwamitin soja, birgadiye-janar Mohamed Toumba, mamba na kwamitin soja ya amsa tambayoyin ’yan jarida game da wannan taro na farko da CNSP ya yi kira da kara jaddada niyyar shugaban nasu ga nacewa wajen neman bakin zare domin ci gaban tattalin arziki da na al’umma, haka tare da kara jan hankali ga wadannan sakatarori da makararrabansu na ma’aikatu da hukumomi da su maida hankali kai da fata wajen tafiyar da hidimomin kasa ba tare da wata matsala ba.

Mamane Ada, sashen hausa na CRI gada Yamai a jamhuriyar Nijar.