logo

HAUSA

NDE ta kammala bayar da horo ga matasa 50 a jihar Bauchi kan harkar noma

2023-07-30 15:28:30 CMG Hausa

Hukumar samar da aikin yi a tarayyar Najeriya NDE ta kawo karshen shirin bayar da horo karo na biyu ga dalibai maza da mata a kan dabarun aikin gona a jihar Bauchi dake arewa maso gabashin Najeriya.

Adadin dalibai 50 da aka zabo daga yankunan kananan hukumomin jihar ne suka amfana da shirin horon, domin su kara samun kwarewa na zahiri a kan abun da tun farko aka koyar da su a cikin aji.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

 

Shirin bayar da horon yana daga cikin matakan da hukumar ke bi wajen samar da ayyukan dogaro da kai ga matasan Najeriya.

Alhaji Aliyu Lawan Yaya shi ne babban jami’in hukumar ta NDE  a jihar ta Bauchi ya yi karin bayani kuma a game da shirin, “Kama mutum ne ya je ya yi digiri, sanann bayan ya kammala kuma a ce ya koma makaranta zai yi masters to wannan bita kamar haka take. A ci gaba ne ga abubuwan da muka koya musu a baya, shi ne wanann muna kiransa Post Sustainable Agricultural Development Program, abun da mutane za su dogara da shi wajen harkar aikin gona. Idan muka ce kuma harkar aikin gona kuma ta kasu kashi-kashi, muna da wadanda suke kula da noma na shinkafa, masara, dawa, gero da sauransu, sannan kuma muna da dalibai wadanda muka koyawa kiwon kifi, kiwon kaji to gaba daya mun tattaro su mun kawo su.”

To ko me daliban za su ce game da wannan horo? Ga abun da wasu daga cikin daliban da suka amfana da shirin bayar da horon suka shaidawa manema labarai.

“Ni ne mai suna Yunis Shukura ina nan a Yelwa. Gaskiya a game da aikin gonar da sun zo su fahimtar da mu akwai karuwa, domin gona yana da amfani, gona kuma shi ne tushen rayuwa. Idan ba noma babu abin da za mu iya yi a cikin kasar, saboda haka ni na yi farin ciki sosai kuma ina neman na koya don ni ma na samu na koyar da wadansu.”

“Sunana Abubakar Aminu. Buri na abun da ya tara mu a nan kullum burinmu shi ne mu samu ilimi yadda za mu yi mu inganta rayuwarmu ko mu rike kanmu da yardar Allah zai kawo hanyoyin da za mu samu jari don a samu damar rage zaman banza da sauransu hakan nan.”

Wasu daga cikin dalibai ke nan da suka samu horo domin bunkasa ayyukansu na noma da kiwo wanda hukumar NDE shiyyar jihar Bauchi ta shirya. (Garba Abdullahi Bagwai)