logo

HAUSA

AU Ta Bukaci Rundunar Sojojin Niger Ta Dawo Da Kundin Tsarin Mulkin Kasar Cikin Kwanaki 15

2023-07-30 16:00:22 CMG Hausa

Kwamitin zaman lafiya da tsaro na kungiyar Tarayyar Afrika wato AUPSC, ya bukaci rundunar sojojin Niger ta dawo da kundin tsarin mulkin kasar cikin kwanaki 15.

Sanarwar da aka wallafa bayan taron kwamitin a ranar Juma’a game da juyin mulkin Niger, ta ruwaito kwamitin na bukatar sojojin Nijer su gaggauta komawa barikinsu ba tare da gindaya sharadi ba, haka kuma su dawo da kundin tsarin mulkin kasar cikin kwanaki 15.

Kwamitin ya kuma yaba da kokarin da kungiyar hadin kan tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka wato ECOWAS ta yi wajen kokarin warware batun.

Haka kuma, kamfanin dillancin labarai na Saudi Press Agency, ya ruwaito shi ma sakatare janar na kungiyar kasashe musulmi ta OIC Hissein Brahim Taha, na yin tir da matakin soji na hambarar da gwamnatin shugaba Mohamed Bazoum a ranar Larabar da ta gabata, da kausasan kalamai, a matsayin Niger na mambar kungiyar OIC.

Cikin wata sanarwa ta gidan talabijin na Niger da yammacin ranar Laraba, dakarun tsaron kasar suka sanar da hambarar da gwamnatin shugaba Bazoum, sa’o’i bayan an yi zargin sun yi garkuwa da shi. (Fa’iza Mustapha)