logo

HAUSA

Gwamnati da rundunar ’yan sanda sun kara daukar sabbin matakan kariya a jihar Sokoto

2023-07-29 15:52:28 CMG Hausa

Gwamnan jihar Sokoto dake arewacin Najeriya Alhaji Ahmad Aliyu ya tabbatar da cewa, sabbin matakan tsaro na hadin gwiwa da jami’an tsaron yankin suka dauka zai taimaka wajen dawo da zaman lafiya a dukkan yankunan dake jihar.

Gwamnan ya tabbatar da hakan ne jiya Juma’a 28 ga wata a Sokoto lokacin da ya karbi bakuncin mataimakin sefeton ’yan sandan Najeriya mai kula da shiyya ta 10 AIG Lawan Abubakar Daura, inda ya ce karuwar ayyukan ’yan ta’adda yana hana wasu daga cikin masu zuba jari zuwa jihar.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto. //////

 

A lokacin ziyarar, mataimakin sefeton ’yan sandan Najeriya shiyya ta 10 ya tabbatar da cewa rundunar ’yan sanda tana daukar batun tsaro a shiyya ta Sokoto da muhimmancin gaske, a kan haka ne a kullum ake bullo da wasu sabbin daburun sirri wajen tarwatsa sansanonin ’yan ta’adda tare kuma da kame masu baiwa ’yan ta’addar bayanai.

AIG Lawan Abubakar Daura ya ci gaba da cewa,

“Ni a matsayina na AIG dole ne za mu duba mu tabbatar da cewa an kare hakkin jama’a , in dai da hadin kan jama’a da kuma fahimta to in Allah ya yarda za a cimma buri, sannan ita kuma gwamnati akwai abubuwa da yawa da ya kamata ta yi mataki mataki na taimakawa al’umma a kowanne fanni. Idan ta taimaka za a rage kaifin talaucin da ake ciki a jihar.”

A lokacin da yake ganawa da manema labarai bayan kammala zaman sirri da mataimakin sefeton ’yan sandan shiyya ta 10, gwamnan jihar Sokoto Alhaji Ahmad Aliyu ya ce, gwamnatin jihar na bakin kokarinta wajen cimma bukatun jami’an tsaron dake jihar a yakin da suke yi da masu tada kayar baya.

“Abubuwan da ake ba su wannan goyon baya ga sha’anin tsaro ba abubuwa ne da za a zo a fada ma al’umma hidi da hidima, saboda su wadannan mutane masu fada ta’addanci su bi hanyoyin da suka samu wasu mutanen wadanda za su rika kusa da mu, mu samu bayaninka, haka ba za mu fadi ba. Amma dai duk da haka a shirye muke mu baiwa jami’an tsaron jihar duk wata gudummawa da suke bukata wajen tabbatar da tsaro a wannan jiha.”

An dai shafe shekaru masana ke kiraye-kirayen a yi hadaka tsakanin gwamnatocin jahohi da jami’an tsaro da kuma al’umma domin kawo karshen matsalar tsaro a jihar Sokoto, matsalar da ta yi sanadiyar mutuwar dubban al’umma domin muddin babu hadin kai a tsakanin wadannan bangarori guda uku za a dauki lokaci kafin dai a kai ga cimma nasarar da ake nema. (Garba Abdullahi Bagwai)